All content for HausaRadio.net is the property of HausaRadio.net and is served directly from their servers
with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.
A yau ne a Najeriya aka shirya soma rarraba kayan aiki don zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ranar Asabar.
Suma masu sa ido, sun buɗe sansaninsu a yau.
Wani kuma, wanda da alama ya fi kowa niyar zaɓen, tun jiya ya isa rumfar zaɓen. Inda yake shirin yin kwanaki uku yana jira kafin a soma kaɗa ƙuri'a."Tun jiya, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi (11:30) na bar gida na. Na tattara kayana, na zo na zauna. Zan yi alƙawari kwana uku.
EU: Tarayar Turai ta kammala wani tsari na wata doka, wadda ta shafi haƙƙin mallaka a intanet. Sai dai, akwai masu ƙorafi akan haka. Za mu ji ko su wanene.