All content for HausaRadio.net is the property of HausaRadio.net and is served directly from their servers
with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.
Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba.
USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri.
USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga.
USA: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar rage tallafin soji da Amurka ke baiwa gamayyar sojojin da Saudiya ke jagoranta a yaƙin Yemen.
Nigeria Elections 2019: Manyan 'yan takarar shugabancin Najeriya, sun sake jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla.
Nigeria: Gwamnar jihar Borno, Kashim Shettima, ya tsallake rijiya da baya a ƙauyen Lugumanu*."Mu mun ɗauka sojoji ne, ashe ba sojoji ba ne. Suna da kayan sarki kuma dukansu sun more..."