A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu. Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu...
Show more...