Home
Categories
EXPLORE
True Crime
Comedy
Business
Society & Culture
Sports
History
News
About Us
Contact Us
Copyright
© 2024 PodJoint
00:00 / 00:00
Sign in

or

Don't have an account?
Sign up
Forgot password
https://is1-ssl.mzstatic.com/image/thumb/Podcasts112/v4/28/8f/f6/288ff628-3cbf-7f54-bd46-95e2f66d171b/mza_6660168502305428375.jpg/600x600bb.jpg
Kasuwanci
RFI Hausa
24 episodes
1 week ago

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Show more...
Business
RSS
All content for Kasuwanci is the property of RFI Hausa and is served directly from their servers with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Show more...
Business
Episodes (20/24)
Kasuwanci
Hangen masana tattalin arziƙi kan sabon harajin gwamnatin Najeriya
Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta.
Show more...
1 week ago
10 minutes 15 seconds

Kasuwanci
Abubuwan da sabon tsarin harajin Najeriya ya ƙunsa
A wannan mako shirin zai tattauna ne kan sabuwar dokar harajin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa hannu, wadda kamar yadda na ambata ba da jimawa, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan gobe na shekara mai zuwa. Tun a watan Yunin da ya gabata shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar harajin da ake sa ran za ta sauya fasalin tsarin karɓa da tattara kuɗaɗen shiga ga gwamnati daga ɓangaren haraji a Tarayyar Najeriya.
Show more...
2 weeks ago
10 minutes 7 seconds

Kasuwanci
Al'ummar Nijar sun rungumi tsarin hada hadar kuɗi ta manhajar waya
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen ƙasar ta Nijar.
Show more...
3 weeks ago
10 minutes 4 seconds

Kasuwanci
Yan Najeriya na yawaba Hasetins kan kafa kamfanin ma'adanai mafi girma a Afirka
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan gina katafaren kamfanin tono da kuma sarrafa ƙarafu da duwatsu masu daraja da wani matashi ya ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, irinsa mafi girma a Afirka, wanda zai laƙume dalar Amurka miliyan 400.
Show more...
1 month ago
10 minutes 6 seconds

Kasuwanci
Shin yaya harajin da bankuna ke cirewa ƴan Najeriya a asusunsu ke shafar tattalin arziki
Shirin Kasuwa a kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan binciken da majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar bayan ƙorafin ƴan ƙasar game da yawan haraji da bankuna ke cirewa a asusun su na ajiya.
Show more...
1 month ago
10 minutes 41 seconds

Kasuwanci
Majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan yawaitar harajin Bankuna
A 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan karon, ya mayar da hanhali ne kan binciken da Majalisar Walikan Nigeria ta ƙaddamar dangane da ƙorafin ƴan ƙasar kan maban-banta haraji da Bankuna ke yawaita cirewa a asusun ajiyarsu.
Show more...
1 month ago
10 minutes 40 seconds

Kasuwanci
Tasirin ƙarin harajin kashi 15 da Najeriya ta sanya kan man da ake shigarwa ƙasar
Shirin a wannan makon ya yi dubi ne akan batun sabon harajin kashi 15 da gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanya kan tataccen man fetur da dangogin sa da ake shigo da su ƙasar daga ketare, ala’marin da ya fara jefa fargaba a zukatan ƴan ƙasar kan yuwuwar tashin farashin litar man na fetur.
Show more...
2 months ago
10 minutes 7 seconds

Kasuwanci
Masana a kan cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ke ɗaukar nauyin ta’addanci
Shirin a wannan makon ya yi dubi ne kan zare sunan Najeriya da cibiyar da ke sanya idanu kan almundahanar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta’addanci a duniya ta yi cikin baƙin kundinta.  A makon da ya gabata ne, Cibiyar nan ta Yaƙi da Masu Safarar Kuɗi da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci ta duniya (FATF), ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da take ɗaukarsu a matsayin masu wanan ɗabi’a.
Show more...
2 months ago
10 minutes 15 seconds

Kasuwanci
An gudanar da taron ƙoli don bunƙasa zuba jari da harkokin kasuwanci a Najeriya
A wannan makon shirin na 'Kasuwa Akai Miki Dole' tare Ahmed Abba zai tattauna ne kan taron ƙoli na ƙasa da ƙasa domin bunƙasa zuba jari da harkokin kasuwanci na farko da jihar Bauchi da ke tarayyar Najeriya ta karɓi baƙunci. Ɗaya daga cikin matsaloli da ke nakasa ci gaban harkokin kasuwanci a Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa ita ce matsalar janyewar masu zuba jari daga fagen harkokin kasuwanci, saboda haka ne ma gwamnatin jihar Bauchi da ke yankin arewacin Najeriya ta shirya wannan taro kan zuba jari irin sa na farko a tarihi.
Show more...
2 months ago
10 minutes 11 seconds

Kasuwanci
Yadda ɗimbin matasan Najeriya masu sana'o'in hannu ke ƙaura zuwa Nijar
A wannan makon shirin na Kasuwa Akai Miki Dole tare Abdulƙadir Haladu Kiyawa zai tattauna ne a kan yawaitar matasan Najeriya masu muhimman sana’o’in hannu da ke yin ƙaura ko kuma tafiya ci rani zuwa wasu ƙasashen Afrika domin neman na rufin asiri, abin da ake alaƙantawa da dalilai da dama da ke sanya matasan ficewa daga ƙasar tasu ta haihuwa.
Show more...
2 months ago
10 minutes 5 seconds

Kasuwanci
Yadda Najeriya ta kashe kusan Dalar Amurka biliyan 3 wajen biyan kuɗin ruwan
Shirin ‘Kasuwa A Kai Miki Dole’ na wannan mako zai tattauna ne kan wasu alƙaluma da suka nuna yadda Najeriya ta Kashe Dala Biliyan 2.86 a cikin watanni 8 na farkon shekarar da muke ciki ta 2025, wajen Biyan Kuɗin Ruwan Basukan da ta karɓo daga ƙasashen ƙetare tare da Nura Ado Suleiman.....
Show more...
3 months ago
10 minutes 3 seconds

Kasuwanci
Yadda ake gudanar da hada-hadar kayayyakin da ake samu albarkacin damuna
Shirin kasuwa a Kai miki dole na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake gudanar da hada-hadar kayayyakin amfanin gona da ake samu a damina,waɗanda ake shukawa da sauran tsirrai da ake samu a daji saboda saukar ruwan sama.Ɗaya daga cikin falalar ruwa ita ce Allah ya rayar da amfanin gona.Da zarar damina ta yi nisa kayan amfanin gona da sauran tsirrai da ba shukasu aka yi ba, suka fara yabaya, to daga nan za’a fara ganin hada-hadar waɗannan kayayyaki irinsu ɗanyar masara,wake, gujiya,da wasu ƴaƴan itatuwa da ake samu a wannan lokaci kadai, harma halitu irinsu Fara.
Show more...
3 months ago
10 minutes 10 seconds

Kasuwanci
Ƙarƙashin mulkin Tinubu Gwamnoni na samun ninkin kuɗaɗen da ake basu a baya
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya dubi batun ƙarin da aka samu a rabon arzikin ƙasa na wata-wata da gwamnatin Najeriya ke yi tsakaninta da jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar, inda alƙaluma su ka nuna yadda wannan kaso ya ƙaru da ninkin abin da aka saba rabawa a baya, tun bayan zuwan wannan gwamnati ta shugaba Bola Tinubu a shekarar 2023.
Show more...
3 months ago
10 minutes 18 seconds

Kasuwanci
Yadda ake ƙara samun saukar farashin kayayyakin masarufi a sassan Najeriya
Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ake ƙara samun raguwar kayayyakin masrufi a Najeriya. Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, tace watanni biyar jere kenan, ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, inda tace an samu sauƙar farashin kayyaki a watan Agustan da ya wuce, da kaso 1 da ɗigo 76 cikin 100, wanda hakan ke nuna yadda aka samu sauƙi fiye da kaso 21.88 na watan Yuli, yayin da yanzu kuma ya koma kaso 20.12 cikin 100.
Show more...
3 months ago
11 minutes 2 seconds

Kasuwanci
Matakin babban bankin Najeriya game da ƙaruwar ayyukan damfara a tashohin POS
Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin Babban bankin Najeriya CBN da ya umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su sanya na’urar bin diddigi ta taswira wato GPS a tashoshin POS a fadin ƙasar, a wani mataki na dakile ɓata gari a bangarori daban-daban masamman ma ayyukan ƴan damfara.
Show more...
3 months ago
10 minutes 13 seconds

Kasuwanci
Yadda faduwar darajar naira ta taimaka wa ƴan Najeriya da ke safara zuwa Nijar
Shirin kasuwa akai miki Dole na wanan makon tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa ya mayar da hankali ne kan yadda karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, ke ci gaba da haɓaka tattalin arziƙin ƙasashen da ke maƙwabtaka ita waɗanda ke amfani da kuɗin CFA.
Show more...
4 months ago
9 minutes 49 seconds

Kasuwanci
Kaso mai yawa na kamfanonin sarrafa shinkafa sun durƙushe a Najeriya
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, zai tattauna ne kan ƙalubalen da ake fuskanta na durƙushewar kamfanonin sarrafa shinkafa a Najeriya, duk da zuba jarin dubban biliyoyin Naira da ‘yan kasuwa suka yi wajen kafa kamfanonin sarrafa shinkafar, waɗanda rahotanni suka tabbatar da cewa an rurrufe da dama daga cikin kamfanonin ko kuma an rage adadin shinkafar da su ke sarrafawa.
Show more...
4 months ago
10 minutes 5 seconds

Kasuwanci
Gwamnatin Najeriya ta fara yunkurin farfaɗo da masaƙun da suka durƙushe
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yunkurin da gwamnatin Najeriya Ke yi na ganin ta farfado da tattalin arzikinta, ta hanyar tada masana'antun da suka durƙushe.  Ƙaramin ministan kasuwanci na ƙasar Sanata John Owan  Enoh ya fara ziyarar wasu daga cikin masakun da suka durƙushe domin ganin sun dawo bakin aiki.
Show more...
4 months ago
9 minutes 57 seconds

Kasuwanci
Takardar kuɗin Najeriya ta samu tagomashi a kwanakinnan
To kamar yadda akaji a matashiyar shirin, ra’ayoyin masana tattalin arziki sun banbanta a Najeriya, tun bayan da sananne a harkar tattalin arziki Bismark Rewane ya tabbatar cewa Naira ta daidaita tsakanin 1500 zuwa 1560 kan kowace dala a makonnin baya-bayan nan, yayin da tattalin arzikin ƙasar kuwa ya fara farfadowa sakamakon matakin babban bankin na Najeriya CBN da ya sanya zunzurutun ƙudi har dalar Amurka biliyan 4 da miliyan 100 cikin watanni shida na wannan shekara...ta 2025.
Show more...
5 months ago
10 minutes 2 seconds

Kasuwanci
Tasirin sabuwar dokar harajin da Tinubu ya sanyawa hannu ga ƴan Najeriya
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan sabuwar dokar Harajin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu a ƙarshen watan Yunin wannan shekara ta 2025 a matsayin wata sabuwar dokar haraji da za ta taimaka wajen sake yi wa tsarin tattara harajin ƙasar garambawul kamar yadda su ka bayyana. 
Show more...
6 months ago
9 minutes 57 seconds

Kasuwanci

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.