Home
Categories
EXPLORE
Comedy
Society & Culture
News
History
Business
Sports
True Crime
About Us
Contact Us
Copyright
© 2024 PodJoint
00:00 / 00:00
Sign in

or

Don't have an account?
Sign up
Forgot password
https://is1-ssl.mzstatic.com/image/thumb/Podcasts122/v4/18/14/29/18142935-1f6c-6912-e323-bad924c24660/mza_4965030127672760520.jpg/600x600bb.jpg
Lafiya Jari ce
RFI Hausa
24 episodes
22 hours ago

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Show more...
Science
RSS
All content for Lafiya Jari ce is the property of RFI Hausa and is served directly from their servers with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Show more...
Science
Episodes (20/24)
Lafiya Jari ce
Fahimtar ƙwararru game da tasirin Hamma ga lafiyar ɗan adam
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir a wannan makon ya mayar da hankali kan wasu daga cikin ɗabi’un jikin ɗan adam da kan faru ba tare da shiri ba, cikin waɗannan ɗabi’u kuwa har da hamma, inda shirin zai duba tasirinta ga lafiyar ɗan adam.
Show more...
4 days ago
9 minutes 53 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda cutar Suga ke mamaya a ƙasashen Afrika
Shirin lafiya jari ce na wannan mao ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da ke cewa mutane akalla miliyan 24 ne ke fama da cutar Suga a Nahiyar Afrika kawai.
Show more...
1 week ago
10 minutes 8 seconds

Lafiya Jari ce
Mutane fiye da dubu 28 na mutuwa duk shekara saboda gurɓacewar iska a Ghana
A wannan makon shirin Lafiya jari ce ya mayar da hankali kan wani bincike a Ghana da ke nuna yadda mutane sama da dubu 28 ke mutuwa duk shekara saboda gurbacewar iska.
Show more...
2 weeks ago
10 minutes 14 seconds

Lafiya Jari ce
Akwai alaƙar mai ƙarfi tsakanin cutar yunwa da taɓuwar ƙwaƙwalwa
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan alaƙar cutar yunwa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa, inda a cikin shirin zakuji yadda masana a ɓangaren suka alakantawa waɗannan matsaloli biyu a matsayin lalurori masu tafiya kafaɗa da kafaɗa da juna.
Show more...
1 month ago
10 minutes 4 seconds

Lafiya Jari ce
An gudanar da gangamin wayar da kai akan cutar daji a Jamhuriyar Nijar
Kowanne watan Oktoba, lokaci ne da ɓangarorin lafiya a Jamhuriyyar Nijar ke amfani da shi wajen gudanar da gangamin wayar da kai a ƙasa baki ɗaya game da cutar sankara ko kuma Cancer wadda ake ganin ƙaruwar masu kamuwa da ita a sassan wannan ƙasa ta yankin Sahel,,,, wannan shi ne maudu’in da shirin na Lafiya jari ce zai mayar da hankali akai sai ku biyomu.
Show more...
1 month ago
10 minutes 5 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda Cholera ta kashe mutane kusan dubu 5 a sassan Najeriya cikin shekaru 5
Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan yawaitar samun cutar Kwalara ko kuma amai da gudawa  a sassan Najeriya, cutar da a baya-bayan nan ta kashe ɗimbin al'umma a ƙasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Afrika. Wasu alƙaluma da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar NCDC ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin dubu biyar (5,000) cutar ta kwalara ta halaka a sassan Najeriyar daga shekarar 2020 zuwa 2025 da muke ciki.
Show more...
1 month ago
10 minutes 26 seconds

Lafiya Jari ce
Cutar Hanta ta Hepatitis nau'in B na yaɗuwa kamar wutar daji a Najeriya
Shirin a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan ciwon hanta nau’in B ko kuma Hepatitis B a turanci, cutar da masana ke gargaɗi game da yadda ta ke yaɗuwa kamar wutar daji tsakanin jama’a.
Show more...
1 month ago
10 minutes 12 seconds

Lafiya Jari ce
Matsalar mace-macen mata a lokacin haihuwa ta ta'azzara a jihar Kaduna
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu  ya mayar da hankali yadda wasu alƙaluman baya-bayan nan a jihar Kaduna ta Najeriya ke nuna yadda ake samun ƙaruwar matan da ke mutuwa yayin goyon ciki ko haihuwa, wanda ke da nasaba da yadda jama’a ke ƙauracewa asibitoci walau a lokacin awo ko kuma haihuwa, wannan shi ne maudu’inmu na wannan mako sai ku biyomu.
Show more...
2 months ago
10 minutes 4 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda yakamata a tunƙari cutukan da ke yawaita a lokacin damuna
Shirin na Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda ake ganin yawaitar jinyace-jinyace mabanbanta da kan kwantar da jama’a kama daga mashasshara ko mura ko kuma ƙurajen jiki dama wasu nau’in cutukan daban-daban, musamman ga ƙananan yara a lokacin damuna.
Show more...
2 months ago
10 minutes 17 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda jama’a suka fi zuwa shagunan saida magani na bakin titi maimakon asibiti
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu, ya maida hankali ne kan yadda jama’a suka fi yadda da shagunan sayar da magunguna na bakin titi wato Chemist, maimakon zuwa asibiti domin ganin Likita.....
Show more...
2 months ago
9 minutes 58 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda Jamhuriyyar Nijar ke ganin yawaitar yaran da ke fama da Tamowa
Shirin lafiya jari ce a wannan mako ya leƙa Jamhuriyar Nijar, inda a dai dai lokacin da ake ganin yawaitar ƙananan yaran da ke fama da cutar yunwa sanadiyyar ƙarancin abinci mai gina jiki da ake kira ƙwamuso a sassan jamhuriyar Nijar, wata matsala da ke tunƙaro shirin yaƙi ko kuma taimakon masu fama da lalurar shi ne yadda ake karkatar da abincin da aka tanadar dominsu.............
Show more...
2 months ago
9 minutes 55 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda mata a Najeriya suka rungumi hanyoyin gargajiya wajan yin tazarar haihuwa
Shirin Lafiya jarice ce na wanan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne a kan hanyoyin gagajiya da mata ke bi wajan sanya tazara tsakanin wannan  da waccen haihuwa.
Show more...
2 months ago
10 minutes 12 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda shirin tallafi ga masu cutar ƙoda zai amfanar da ɗimbin jama'ar Najeriya
Shirin Lafiya Jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin Najeriya na rage farashin wankin ƙoda ko kuma Dialysis, daga Naira dubu Hamsin ko fiye da haka zuwa Naira dubu 12 kacal.
Show more...
3 months ago
9 minutes 49 seconds

Lafiya Jari ce
Asusun UNICEF ya koka kan ƙaruwar ƙananan yara da ke fama da yunwa a Najeriya
Shirin 'Lafiya Jari Ce' a wannan mako, ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki akan wani rahoton Asusun kula da ƙananan yara na Majlisar Ɗinkin Duniya UNICEF, wanda ya bayyana ƙaruwar adadin yaran da ke fama da yunwa ko kuma ƙarancin sinadaran abinci masu gina jiki a wasu sassan arewacin Najeriya.
Show more...
3 months ago
9 minutes 59 seconds

Lafiya Jari ce
Muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah a watannin shidan farko
  A wannan makon shirin ya yi duba kan tsarin nan na shayar da nonon uwa zalla ga jarirai tun daga haihuwa har zuwa watanni 6 ba tare da silki ba, tsarin da ake cigaba da ganin mabanbantan ra’ayoyi hatta daga iyaye dama wasu jami’an lafiya.
Show more...
3 months ago
10 minutes 1 second

Lafiya Jari ce
Matakin Amurka ka iya haifar da koma baya ga shirin yaki da cutar HIV a Najeriya
Shirin ya mayar da hankali ne kan yadda matakin Amurka na janye tallafin da take ba wa ɓangaren kula da masu fama da cuta mai karya garkuwa jiki ta HIV da ake fargabar zai iya haifar da koma baya ga shirin yaƙi da cutar.
Show more...
3 months ago
10 minutes 11 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda matsalolin tsaro ke haddasa ƙarancin abinci da ke assasa cutukan yunwa
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba kan yadda matsalolin tsaro ke haddasa ƙarancin abinci wanda ke matsayin masabbabin cutuka masu alaƙa da yunwa musamman a yankunan jihohin Sokoto da Zamfara da matsalolin ƴanbindiga suka zama ruwan dare.
Show more...
4 months ago
9 minutes 54 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda za a magance matsalar ficewar Likitocin Najeriya ƙetare
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakan da ya kamata a ɗauka don daƙile ficewar likitocin Najeriya zuwa ƙetare, wanda ke kassara ɓangaren lafiyar ƙasar ta yammacin Afrika.
Show more...
4 months ago
9 minutes 29 seconds

Lafiya Jari ce
Uku cikin Ma'aurata goma a Najeriya na fama da matsalar haihuwa - Rahoto
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani binciken ƙwararru da ke nuna cewa duk 3 cikin ma’aurata 10 a Najeriya na fama da matsalar haihuwa, alƙaluman da ke nuna tsanantar matsalar a wannan ƙasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika.
Show more...
5 months ago
9 minutes 53 seconds

Lafiya Jari ce
Yadda Najeriya ta tashi tsaye wajen yaƙi da cutar kansar bakin mahaifa
Shirin Lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluman baya-bayan nan da ke nuna yadda mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa ko kuma cervical cancer duk shekara a Najeriya, alƙaluman da ke da matuƙar tayar da hankali, ganin yadda wannan cuta ke kisa ba ƙaƙƙautawa ga duk waɗanda suka kamu da ita.
Show more...
5 months ago
9 minutes 7 seconds

Lafiya Jari ce

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.