Na sami zama tare da Lauya Dan Gwagwarmaya Barrister Solomon Dalung, tsohon Ministan Matasa Da Wasanni a lokacin mulkin Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari. Inda na tattauna da shi don kallon rayuwarsa a cikin shirin Madubin Usman Kabara Podcast domin daukar darasi ga ‘yan baya.
Na ziyarci Usman Umar (SojaBoy), domin yin hira da shi ido da ido a kokarina na jin dalilan salon wakokinsa da mafiya yawan mutane musamman 'yan Arewacin Najeriya, ba su yarda da salon nasa ba, suna ma kallon abin a matsayin rashin tarbiyya da rushe al'ada da addini.
Nazir Ahmed Hausawa (Ziriums), yana daya daga cikin ‘yan masana’antar finafinan Kannywood, Makadin Fiyano, Mawakin gambarar Hausa HipHop, Tsohon malamin koyar da kida, Tsohon ma’aikacin BBC World Service Trust da VOA Hausa, Masanin harkokin gidajen alfama na Amurka. A cikin hirarsa da Madubin Usman Kabara a Amurka, ya bayyana min darussan da ya koya a zamansa na shekaru a Amurka.
Na sami yin hira da shahararriyar Jarumar Fina-finan Hausa Nafisat Abdullahi a birnin Washington DC da ke Amurka, don sanin asalinta da kuma yadda take tafiyar da rayuwarta.
Na yi hira da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Mai Girma Sanata Barau I. Jibrin (Maliya) game da rayuwarsa da kuma gudunmawarsa a siyasance, musamman ga 'yan Arewacin Najeriya.
Kamaluddeen Kabir, dan asalin jigar Katsina ne mai digirin digirgir wanda yayi karatunsa a tsakanin Najeriya da Birtaniya sannan kuma Malami ne yanzu haka a jami'ar Umaru Musa 'YarAdua da ke jihar ta Katsina.
Mun sami tattaunawa Aminu Waziri Tambuwal gwamnan jihar Sokoto, kuma shugaban tawagar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya a 2023 da ke tafe. Inda ya bamu labarin kuruciyarsa har zuwa girma da shiga fagen siyasa. Ba mu bar shi ba sai da ya fada mana dalilinsa na janye wa daga takarar shugabancin Najeriya don mara wa Atikun a karkashin jam'iyyar PDP.
Na'ima Idris Usman, cikakkiyar Likita ce da ke jihar Kanon Najeriya, ta yi karatun a tsakanin Najeriys da China. Ta bamu labarin rayuwarta daga kuruciya zuwa girmanta, da ma yadda aka yi ta fara ilimantar da mata ta kafafen sada zumunta game da lafiyar jikinsu duk da cewa furta kalmomin da ke da alaka da al'aura abu ne mai cike da kalubalen a kasar Hausa. Da kuma yadda karshe ta buge da zuwa shirin horar da shugabanci ga matasan Afirka a Amurka da a turance ake kira da Mandela Washington Fellowship da aka fi sani da Young African Leaders Initiative (YALI) na shekarar 2022.
Usman Umar da aka fi sani da Soja Boy mawaki ne, dan wasan kwaikwayon zahirin rayuwa da ya fito a tauraron wani shirin wasan talbijin a Amurka mai suna 90DayFiance wanda ake bibiyar saurayi da budurwa don ganin yadda alakarsu ta soyayya ke tafiya.
Aisha Hassan matashiya ce 'yar asalin jihar Neja a Najeriya da ta girma a Ingila, sannan ta yi karatu mai zurfi a fannin hada-hadar kasuwanci. Bugu da kari ba a barta a baya ba wajen shiga fagen kafafen sadarwar zamani inda take koyar da salon sa sutura da daurin dan-kwali a shafukanta na yanar gizo.
An karrama Halima Ali Shuwa da lambar yabon gama digirin digirgir a matsayin dalibar da ta yi wa sa’o’inta fintinkau a fanni binciken sojojin garkuwar jikin bil’adama. Bugu da kari kuma sai ga wani babban kamfanin hada magunguna a duniya ya bata aiki sakamakon fahimtar amfanin abin da ta kware a fannin binciken kwayar halitta.
Adamu Garba II matashi ne mai kwarin gwiwa sannan wanda ya ke dan kasuwar da yayi iliminsa a tsakanin Najeriya har zuwa Amurka. Yana daga cikin 'yan takarar Shugaban Kasar Najeriya a shekarar 2023 mafi karancin shekaru a tsakanin masu neman wannan kujera a kasar da ta fi kowa ce kasar Afirka yawan al'umma da kuma karfin arzikin man fetur. Shine kuma wanda 'yan uwa da abokan arziki suka tara wa sama da naira miliyan 80 don yin takara a jam'iyyar APC amma kwatsam sai ya canja sheka zuwa YPP.
Mu'awiya Said Abdullahi, ya yi karatu ne a fannin zanen gidaje da kuma tsara birane. An haifeshi ne a garin Kaduna, sannan iyayensa Lauyoyi ne. Ya fara digirinsa ne daga jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ya kuma kammala a daya daga jami’o’in kasar Malaysia. Yayi digirinsa na biyu da na uku a Korea ta Kudu, inda yanzu haka ya ke aiki a matsayin shugaban bangaren kula da bangaren tsara biranen kasashen waje a wani babban kamfani a kasar ta Koriya ta Kudu mai suna WithWorks da ke birnin Seoul.
Ibrahim Sherif bakano ne dan Najeriya da ya bar gida tun yana dan saurayi zuwa Birtaniya domin aikin sa kai. Inda daga baya ya nausa Afirka ta Kudu inda ya cika burinsa na zama matukin jirgin sama, har ma ya buge da tsere keke a can.
Dalibi ne da ya ke digirin digirgir a fannin Turanci da fasahar hotunan finafinan majigi. Matashin ya bayyana yadda jin wani shiri a gidan radiyon Muryar Amurka na VOA ya ba shi kaimin neman zuwa karatu a Amurka, har ya buge da koyar da harshen Hausa tun a digirinsa na biyu a wata jami'a ta Amurka.
Wani hazikin matashin likitan dabbobi ne da yake digirin-digirgir a birtaniya, tare da yin binciken a fanni kwayoyin cututtukan dabbobin da kuma gano dalilan da ke hana wasu magungunan dabbobin aiki da ya kamata su yi. Ya bayyana mana tarihin rayuwarsa da ma yadda aka yi yayi digiri na biyu a Turai da ma ci gaba da digirinsa na uku. Ya tabo batun yadda yake ganin noma da kiwo a kasashe kamar Najeriya.
Karatu ne ya kai iyayen Iman Yusuf Al-Hassan zuwa Amurka, wanda su 'yan asalin jihohin Kano da Jigawa ne a Arewacin Najeriya, amma kuma kaddarar zama ta kama su har suka hayayyafa. Iman ta fada min yadda take da burin zaman Najeriya duk kuwa da cewa a Amurka aka haifeta ta girma.
Hadiza Aliyu da aka fi sani da Gabon, na daya daga cikin fitattun taurarin fina-finan Hausa mafi shahara., wacce ta shiga Najeriya a lokacin bata jin Hausa, amma tana son zama tauraruwar fina-finan Hausa na Kannywood. Na yi gajeriyar hira da ita don jin yadda aka yi ta cimma burinta wanda gashi kuma yanzu tana shige da fice a kasashen duniya., inda har tya kawo ziyara ga iyalina da ke Amurka.
Maimuna Sulaiman Bichi da aka fi sani da ‘yar Bichi ko Lolo’s Kitchen ‘yar asalin Najeriya ce ta suka dawo Amurka da zama tun tana shekaru 15 da haihuwa. Ta kuduri aniyar bude gidan abincin da zai kware a girke-girke musamman ma irin na gargajiyar Hausawa.
Binta Aliyu Zurmi da aka fi sani da Elbynt, ‘yar jarida ce daga Najeriya mazauniyar kasar Jamus kuma ma’aikaciya a daya daga fitattun gidajen radiyon Hausa da ke kasashen waje. Ku biyo mu don kallo ko sauraron tattaunawar da muka yi da ita game da tarihin rayuwarta a gida da kasahen waje.