
‘Yar Nijar kuma masaniyar kimiyyar ruwa da doron kasa da ke aiki a hukumar sama-jannatin Amurka ta NASA. Dr. Fadji Maina tana cikin wacce mujallar tereren arziki ta Forbes ta wallafa sunanta a cikin matasan duniya guda 30 ‘yan kasa da shekara 30 da suka sami nasara a rayuwa. Yanzu haka ma’aikaciya ce a hukumar sama jannatin Amurka ta NASA da ke aiki bisa kwarewar ta a fannin ruwa da kimiyyar doron kasa.