
Haruna Salisu wanda aka fi sani da Chizo1 Germany, Mawaki ne kuma Dan Wasan Barkwanci, sannan tauraro ne a shafukan sada zumunta. A cikin wannan hirar tamu ta farko a shirin Madubin Usman Kabara, Chizo ya bani labarin yadda ya bar gida da niyyar shiga kasashen Turai ta kafa don neman mafita a rayuwa, da kuma yadda ya tsinci kansa a Jamus har da auren Bajamushiya farar fata. Yanzu haka har yana da sarautar Sarkin Samarin Turai.