
Imrana matashi ne danye shataf daga jihar Yobe, wanda har yanzu bai shekara talatin da haihuwa ba, sannan ba dan masu kudi ko mulki ba ne, amma ya sami nasararorin rayuwar da har Sarauniyar Ingila sai da ta karrama shi saboda wasu dalilan da matashin ya bayyana a wannan tattaunawa da mu ka yi dashi game da tarihin rayuwarsa.