
Na ziyarci Dr. Sabo Tanimu a jihar Wisconsin ta Amurka. Yana daya daga cikin kwararrun likitocin kayan cikin bil'adama a kasar inda yake shugabantar bangaren cutar dajin da ta shafi kayan ciki. Dan asalin Najeriya ne daga jihar Benue a tsakiyar Arewacin Najeriya. Shin yaya aka yi Likita Sabo ya fara daga Najeriya har ya tsinci kansa a Amurka inda ya shafe shekaru da dama yana aikin Likita a can.