Home
Categories
EXPLORE
True Crime
Comedy
Society & Culture
Business
Sports
TV & Film
Technology
About Us
Contact Us
Copyright
© 2024 PodJoint
00:00 / 00:00
Sign in

or

Don't have an account?
Sign up
Forgot password
https://is1-ssl.mzstatic.com/image/thumb/Podcasts221/v4/b6/6f/72/b66f7251-c078-a8f3-29b4-32bed8298330/mza_9500036076761979941.jpg/600x600bb.jpg
Najeriya a Yau
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim
883 episodes
6 hours ago
Send us a text Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ...
Show more...
News Commentary
News,
Politics
RSS
All content for Najeriya a Yau is the property of Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim and is served directly from their servers with no modification, redirects, or rehosting. The podcast is not affiliated with or endorsed by Podjoint in any way.
Send us a text Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ...
Show more...
News Commentary
News,
Politics
Episodes (20/883)
Najeriya a Yau
Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
Send us a text Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ...
Show more...
6 hours ago
19 minutes

Najeriya a Yau
Matsayar Doka Kan Taron Da Jam'iyyar PDP Ta Gudanar
Send us a text Matsayar doka ta zama babbar abun tattaunawa a Najeriya yayin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron ta na kasa duk da mabanbantan hukunce hukunce daga kotuna biyu. Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce hukunce ba baiwa jam’iyyar damar yi ko haramta musu taron kadai suka yi ba, harda baiwa hukumar zabe ta kasa umurnin saka ido ko haramta musu wannan dama yayin taron. Duk da wadannan hukunce hukunce, jam’iyyar ta gudanar ...
Show more...
3 days ago
25 minutes

Najeriya a Yau
Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani
Send us a text A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani. Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat. Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce? Wannan s...
Show more...
6 days ago
27 minutes

Najeriya a Yau
Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya
Send us a text A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar. Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba kafin wa'adin ...
Show more...
1 week ago
26 minutes

Najeriya a Yau
Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Kungiyar ASUU
Send us a text A yayin da tattaunawa kan makomar ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ke ci gaba da ɗaukar hankali, batun yadda za a haɗa jami’o’i masu zaman kansu cikin tsarin ƙungiyar ya sake tasowa. Wasu na ganin wannan sabon yunƙuri zai iya zama sabuwar hanyar ƙarfafa hadin kai tsakanin malamai, yayin da wasu ke gargadin cewa hakan na iya kawo tsaiko ga karatun wasu dalibai dake kauracewa jami’oin gwamnati sakamakon yawan yajin aiki da suke tsunduma lokaci zuwa lokaci. Wa...
Show more...
1 week ago
25 minutes

Najeriya a Yau
Dalilan Yaduwar Cutuka A Irin Wannan Lokaci
Send us a text Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Show more...
1 week ago
27 minutes

Najeriya a Yau
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
Send us a text Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta. A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tat...
Show more...
2 weeks ago
26 minutes

Najeriya a Yau
Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
Send us a text Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi.  ...
Show more...
2 weeks ago
25 minutes

Najeriya a Yau
Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Send us a text Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro. Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Show more...
2 weeks ago
24 minutes

Najeriya a Yau
Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
Send us a text Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa. Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi. Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba. Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokar...
Show more...
2 weeks ago
24 minutes

Najeriya a Yau
Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya?
Send us a text Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce. Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.
Show more...
3 weeks ago
25 minutes

Najeriya a Yau
Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas?
Send us a text A cikin ‘yan watannin da suka gabata, an sake ganin karuwar hare-haren Boko Haram da ISWAP musamman a yankin Arewa maso Gabas. Kazalika, ko a kwanan nan ma anga irin wadannan hare hare. Wadannan hare-haren sun fi karkata kan sansanonin sojoji, inda ake samun asarar rayuka da dama, da kuma lalata kayan aikin gwamnati. Rahotanni daga Borno da Yobe da ma wasu sassan kasar nan sun nuna yadda ‘yan ta’adda suka sake samun karfi wajen kai hare-hare cikin dare, tare da amfani da daba...
Show more...
3 weeks ago
27 minutes

Najeriya a Yau
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Haraji Da Zai Fara Aiki A 2026
Send us a text A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden shiga da kuma rage dogaro da albarkatun mai. Sai dai, jama’a da dama ba su da cikakken bayani game da irin wadannan sabbin haraji ko menene suke nufi ba. Shin ko ta wadanne hanyoyi ne wannan sabon haraji ...
Show more...
4 weeks ago
24 minutes

Najeriya a Yau
Halin Da Muka Shiga Sakamakon Haihuwar ‘Ya Mai Cutar Motsewar Kwakwalwa
Send us a text Cutar Cerebral Palsy, wadda ake kira Ciwon tsukewar kwakwalwa, na daga cikin manyan matsalolin lafiyar yara da ke tasowa tun daga haihuwa. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon rauni ko lalacewar wani ɓangare na kwakwalwa da ke kula da motsi, magana, da daidaiton jiki. A mafi yawan lokuta, cutar tana bayyana ne tun daga ƙuruciya, a wasu lokutan kuma kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana, cutar na faruwa ne tun kafin a haifi yaro. Ko ta wadanne irin hanyoyi wannan cuta...
Show more...
1 month ago
28 minutes

Najeriya a Yau
Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?
Send us a text Tun bayan fara shari’ar Nnamdi Kanu a shekarar 2021 mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu a kan sake shi ko a kyale shari’a ta yi halinta. Hasali ma har zanga-zanga wasu ‘yan Najeriya suka kira don bayyana bukatar sakin shugaban na ‘yan aware. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ko ya dace a saki Nnamdi Kanu?
Show more...
1 month ago
24 minutes

Najeriya a Yau
Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a
Send us a text Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba. Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin...
Show more...
1 month ago
18 minutes

Najeriya a Yau
Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
Send us a text Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba.
Show more...
1 month ago
23 minutes

Najeriya a Yau
Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa
Send us a text A duk lokacin da a ka samu canjin shugabanci, hakan kan zo da kalubale da dama. Muƙamin shugabancin Hukumar Zabe ta kasa na daga cikin mukamai a Najeriya da 'yan kasa ke cece-kuce a kai. Ko wadanne irin Kalubale ne ke gaban sabon shugaban hukumar zabe ta kasa? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.
Show more...
1 month ago
21 minutes

Najeriya a Yau
Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe
Send us a text A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci. Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsar...
Show more...
1 month ago
27 minutes

Najeriya a Yau
Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma
Send us a text Takardun shaida na bogi na daya daga cikin matsaloli dake kara addabar Najeriya a fannoni da dama. A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun makaranta ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, mukami, ko wasu fa’idodi da suka wajaba ne kawai ga waɗanda suka cancanta. Wannan dabi’a ta zama barazana ga ci gaban ƙasa da amincin al’umma gaba ɗaya, domin tana lalata tsarin ilimi, rage darajar masu gaskiya, da haifar da rashin inganci a wuraren aiki. ...
Show more...
1 month ago
28 minutes

Najeriya a Yau
Send us a text Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai ...